BUA ya bada tallafin tebura 1,000 da kudinsu ya kai N32m ga Makaranta a Sokoto

Advertisements

Kamfanin BUA Cement PLC ya fara rabon teburan mutane 1,000 masu mutum uku da kudinsu ya kai Naira miliyan 32 ga makarantun da ke fadin jihar Sakkwato a ranar Asabar.
A lokacin da daraktan gudanarwa da tallace-tallace na BUA PLC, Abdulganiyu Yusuf yake jawabi ya ce matakin na daga cikin kudirin kamfanin na tallafa wa al’ummar da za su karbi bakuncinsa.
Mista Yusuf ya ce an dauki wannan matakin ne domin jin dadin manufofin gwamnatin jihar Sokoto na ayyana dokar ta baci kan ilimi.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like