Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana sun bayyana cewa Jirgin saman shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ci Naira biliyan 11.13 a shekara 2022.
An kashe kudin ne don kula da jiragen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke amfani da su a shekarar 2022, wanda ke nuna kashi 98 cikin 100 na kudaden da aka amince da su a cikin kasafin kudin.
A ya yin da aka fitar da sanarwar, rundunar ta ce kasafin kudin bai wadatar ba wajen gudanar da ayyukan rundunar, domin ana bukatar wasu dala miliyan 45 don kula da jiragen.