Advertisements
A jiya Juma’a a gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranci hannunta Tsangayar zamani da ya ginawa Almajiran dake karatu a babbar Tsangayar Goni Sani dake unguwar Yelenguruza.
An gina wannan tsangaya ne ƙarƙashin hukumar BESDA wanda Dr. Abdullahi Bappah Garkuwa ke jagoranta, domin inganta karatun Almajirai a jihar.
A cikin katafaren ginin an samar da fannonin koyon sana’a domin rage barace barace ta yadda Almajiri zai kula da kansa. Fannonin sana’a sun hada Dinki, Aski, Hada Takalma Da Dai Sauransu.
Taron ya samu halartan manya manyan baki kama daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar lll, sarakunan gargajiya da kuma manyan masu rike da mukaman gwamnati a matakai daban daban na tarayya.
– Hajji Shehu