Bidiyon Tinubu: Ba cin hanci ba ne Tinubu ya bayar, taimako ne ya bayar ga talakawa

Advertisements

Mataimakiyar mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta bayyana dalilin da ya sa ta saka bidiyon dan takarar jam’iyyar, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima, suna miƙa tsabar kudi na naira ga wani mutum mai rauni a Abuja.
An dauki bidiyo na mintuna biyu ne a ranar Talatar da ta gabata suna ba wa mutumin sabbin takardun kuɗi na Naira a wani taro da aka yi da nakasassu.
A cikin faifan bidiyon dai an ga dan takarar na jam’iyyar APC wanda ya sanya riga mai launin ruwan kasa da kuma shudin hula, inda ya mika hannunsa ga daya daga cikin mukarraban sa, wanda ya ba shi kuɗin da ya mika wa mutumin.
Bidiyon ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta inda masu suka da ‘yan adawa da suka haɗa da Reno Omokri, tsohon mai taimaka wa Shugaba Goodluck Jonathan da Emeka Obasi, mai taimaka wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a kafafen yada labarai, sun bayyana shi a matsayin cin hanci da rashawa.
Da take mayar da martani, Musawa a cikin wata sanarwa ta ce ba adalci ba ne wasu ‘yan Najeriya su bayyana abin tausayi da Tinubu ya nuna a matsayin cin hanci.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like