Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka Babban Bankin Nijeriya CBN ya kara adadin kudaden da ’Yan Najeriya za su Iya cirewa duk mako daya, daga dubu 100 zuwa dubu 500
Babban Bankin Najeriya ya kara adadin tsabar kudi da ‘yan Najeriya za su iya cirewa a asusun banki duk mako zuwa N500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan 5 duk mako.
Wannan karin na zuwa ne a cikin wata wasika da CBN ya aikewa dukkan bankunan kasar nan a ranar Laraba 21 ga watan Disamba, TheCable ta ruwaito. Babban bankin ya yanke wannan shawarin ne bayan sauraran korafe-korafe daga daga masu ruwa da tsaki a Najeriya.