Advertisements
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta inganta aiki da rayuwar ‘yan sandan Najeriya.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya karbi rahoto kan rundunar ‘yan sandan kasar na shekarar 2021, da karbar kudurin kasafin kudin ‘yan sanda na badi.
Sanarwar ta ci ambato shugaba Buhari na cewa: “wannan gwamnatin ta sanya walwala da inganta aikin ‘yan sanda a sahun gaba, kuma hakkinta ne ta kawo sauye-sauye masu inganci a aikinsu.
Ni da kai na na amince muhallin da ‘yan sanda ke zaune a ciki ba mai inganci ba ne, dan haka gwamnatinmu ta kuduri aniyar sauya musu ingantacciyar rayuwa, ba su kadai ba har da sojojin Najeriya,” in ji shugaba Buhari.
Ya kara da da cewa ya san duk lokutan da aka yi wa jami’an tsaro sauyin wurin aiki, ba za su yi dar ba wajen zuwa aikin, saboda sanin sun bar iyalansu cikin ingantaccen muhalli da tsaro a bariki, yara na zuwa makaranta mai kyau, ga asibitoci masu inganci, wannan zai kara musu kwarin gwiwar gudanar da aikinsu yadda ya dace.
Batun karawa ‘yan sanda albashi da walwala ya dade ana tattaunawa a kai a Najeriya, rashin samun albashi da alawus mai tsoka na daga cikin dalilan da ake cewa ya janyo kananan ‘yan sanda karbar na goro.