Cutar Sikila ya yi sanadiyar ‘Yayana biyu har lahira cewar Shugaba Buhari

Advertisements

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiyana ce a ƙalla ‘yayansa biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon cutar Sikila.
Buhari ya ce hakan ne ranar Juma’a a wajen wani gagarumin taro da ‘yan uwa da mutanen arziki suka shirya masa kan bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa a fadarsa.
Yayin da yake jawabi game da rayuwarsa shugaba Buhari ya ce ‘ya’yansa biyu ne – da ya haifa tare da matarsa ta farko mai suna Safinatu – suka rasu sakamakon cutar Sikila.
Ya ƙara da cewa hakan ya tilasta masa yin gwajin ƙwayoyin halitta a lokacin da ya tashi auren matarsa ta yanzu Aisha Buhari.
Ya ce ya dage cewa dole sai matar da zai aura ta kasance tana da ƙwayoyin halitta na AA, don kauce wa ɗaukar cutar Sikila ga ‘yayan da zai haifa kasancewar shi yana da ƙwayoyin halitta na AS.
Buhari ya auri Safinatu a shekarar 1971. sun kuma haifi ‘ya’ya biyar tare da ita.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like