Advertisements
Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kaddamar da bincike kan dalilin da ya sa yadda fitaccen mai dafa abinci Nusret Gokce Salt Bae ya rike kofin duniya a bikin rufe gasar cin kofin duniya ta FIFA.
A cewar rahotanni, za a dau mataki a kan ma’aikatan da suka ba shi damar yin cudanya da tawagar Argentina a filin wasan
Dokokin FIFA sun ce wadanda suka lashe gasar cin kofin duniya da shugabannin kasashe ne kadai aka amince su taba kofin a gasar cin kofin duniya,