Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun tabbatar da cewa Mabiya Shi’a, almajiran Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky, sun ziyarci Coci domin taya al’ummar Kiristoci Murnar Kirsimeti.
Tawagar Mabiyan Shi’a na babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja sun ziyarci Cocin Mararrabar Abuja, domin taya Kiristoci Murnar da samuwar Annabi Isah.
Hakazalika kuma mabiya shi’a da ke garin Yankara da kuma ƙaramar hukumar Danja a jihar Katsina, su ma sun ziyarci Coci domin taya Kiristoci Murnar Kirsimeti.
A wani ɓangaren ma wasu mabiya shi’a mazauna Jalingo jihar Taraba sun ziyarci Coci domin taya Kiristoci Murnar Kirsimeti.