Ƙasar Amurka ta sha Alwashin taimakawa NDLEA domin kama masu ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi

Advertisements

Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta na yin wani shiri domin ƙarfafa wa hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta hanyar inganta binciken kimiyya da na sinadarai da kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Femi Baba Femi ya fitar ranar Litinin ya ce taimakon na Amurka na zuwa ne bayan da shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya buƙaci hakan daga hukumomin na Amurka bayan jerin ganawa da ya yi da manyan jami’an Najeriya da na Amurka.
Baya ga taimako a ɓangaren binciken kimiyya da na sinadaran, gwamnatin ta Amurka ta ce shirin zai taimaka wa hukumar wajen samun hanyoyin tattara bayanan sirri ta hanyar na’urori na zamani.
Matakin na zuwa ne bayan da wata ƙungiya mai suna Abdul Samad Rabiu Initiative (ASR Africa) ta bayar da kyautar naira miliyan 500 ga hukumar ta NDLEA domin ɗaukar nauyin wasu manyan ayyukan hukumar.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like