Abin tausayi wani Matashi mai suna Salisu Husaini ya rasa Hannunsa sanadiyyar rabon Faɗa

Advertisements

Salisu Hussaini, wani wanda yayi kokarin kwantar da tarzoma ta hanyar tsaida rikicin da ya barke tsakanin.
 Makwabtansa biyu ya rasa hannunsa sanadin hakan Hakan ya biyo baya ne yayin da matashin mai shekaru 21 yayi kokarin raba fadan inda daya daga cikinsu yayi kokarin soka masa wuka a ciki, amma ya kare a hannunsa.
 Telan wanda asibitin kashi na Dala ta yanke hannunsa da ya rube bayan kamuwa da cutar Tetanus, yayi kira ga hukumomi da su kwatar masa ‘yancinsa.
Matashi Salisu bai taba sanin sasanci da tsaida kwantar da tarzoma da shiga tsakanin makwabtansa 2 a Kano zaiyi sanadiyyar nakasarsa ba ta hanyar da bai yi tsammani ba. 
Lamarin wanda ya auku a yankin Fagge cikin garin Kano yayi sanadiyyar da Husaini, matashin mai shekaru ashirin da daya yayi rashin hannunsa sakamakon soka masa wuka da wani hatsabibi, Abubakar Ayuba, da ake kira da Namama a yankin yayi. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like