Advertisements
Babbar Jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsin-ma jihar Katsina ta sanar da karin kudin makaranta ga dukkan daliban ta daga zangon karatu na 2022/2023.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar Magatakardan jami’ar kuma Sakataren majalisar koli ta jami’ar, Iliyasu S. Falalu.
A cewar sanarwar, jami’ar za ta cigaba da tsarin bayar da dama ga daliban jami’ar su rika raba biyan kudin makarantar
zuwa sau biyu a zango daya idan da bukatar hakan.
Kamar yadda Katsina Post ta samu kundin dake dauke da karin kudin, dalibai yan Najeriya a makarantar za su biya kudin da suka kama daga N252,000 ga sabbin daliban digirin digir-gir har zuwa N11,3000 ga wasu daliban digiri na farko a jami’ar.
Ga dai jadawalin nan a kasa: