YANZU-YANZU: Akwai yiwuwar sake baɗawa sabon hare-hare tsakanin Ukraine da Rasha

Advertisements

Kasar Ukraine ta bayyana tsoronta ga yadda kasar Rasha ke shirin kawo mata sabbin hare-hare a ‘yan kwanakin nan.
 An ce kasar Rasha ta siyo manyan makamai daga kasar Iran, kuma a haka ne za ta kai hari don wargaza kasar An fara fada tsakanin Ukraine da Rasha tun a wata Fabrairu, ana kare jini biri jini tsakanin kasashen biyu.
Kyiv, Ukraine – Kasar Rasha na shirin kai munanan hare-haren kan kasar Ukraine a ‘yan kwanakin nan masu zuwa, a cewar shugaba Zelensky na kasar ta Ukraine. A cewarsa, Rasha za ta yi amfani da wasu nau’ikan kananan jirage marasa matuka don aiwatar a shirin wargaza kasar ta Ukraine mai makwabtaka da Rasha.
A cewar Zelensky, ya samu bayanan sirri daga Rasha kan wannan shiri na hare-hare, kuma kasar Iran ne ta kera jiragen da Rashan za ta yi amfani dasu, inji rahoton BBC Hausa.
Ukraine ta yi ikrarin hallaka sojojin Rasha Idan baku manta ba, kasar Ukraine ta yi ikrarin kai hari kan dakarun Rasha a yankin Donbas, inda tace ta kashe daruruwansu a sabon harin.
A gefe guda, Rasha ta musanta wannan ikrari tare da cewa, an kashe dakarunta 63 ne kacal a wannan harin, NDTV ta tattaro. A sabon batunsa, Zelensky ya koka da cewa, Rasha na shirin ‘wargaza’ Ukraine a sabbin hare-haren da take da shirin kaiwa kasar. 
Ya bayyana wannan zargin ne a birnin Kyiv a daren jiyar Litinin 2 ga watan Janairu yayin da yake magana da duniya baki daya. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like