ABUN A YABA: Abdulsamad BUA Ya Bawa Jami’ar Al-Qalam Tallafin Naira Miliyan 250

Advertisements

Shahararren Mai Kudin Afrika Abdulsamad BUA ya bawa Jami’ar Al-kalam Katsina Tallafin Naira Miliyan 250

Jami’ar Al-Qalam Katsina ta yaba wa shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi’u bisa bayar da tallafin samar da ababen more rayuwa na kimanin Naira miliyan 250 ga jami’ar dake cikin birnin Katsina.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Nasiru Yauri, ya yi wannan yabon ne a cikin wata sanarwa da kansa ya sanya wa hannu kuma ya bayyana wa manema labarai a ranar Litamin ɗin da ta gabata a Sokoto.

Advertisements

A cewar Mista Yauri, tallafin da aka bayar ta hanyar Abdulsamad Rabiu Africa Initiative, ASR Africa, yana da matuƙar tasiri wajen magance taɓarɓarewar ababen more rayuwa a manyan makarantun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like