ABIN TAUSAYI: mutum 18 su kone ƙurmus a sakamakon Hatsarin mota a jihar Bauchi

Advertisements

Mutum aƙalla 18 ne suka ƙone ƙurmus sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda motar bas ta yi taho-mu-gama da tirela ranar Laraba. 
Kwamandan ya ce hatsarin ya ƙunshi motar bas ƙirar Toyota Hiace da kuma babbar mota, wadda mutum uku da ke cikinta ba su ji ko ƙwazane ba.
A cewarsa, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:40 na yamma, kuma jami’an hukumar sun isa wurin cikin minti bakwai da faruwarsa.
Ya ɗora alhakin hatsarin kan gudun wuce sa’a wanda ya haddasa motocin biyu suka yi karo da juna.
“Mutum 21 ne abin ya ritsa da su kuma akwai manya 18 da yara uku. !8 ɗin suna cikin bas ɗin kuma sun ƙone ƙurmus bayan ta kama da wuta sakamakon karon da ta yi da tirelar,” in ji shi.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like