Advertisements
Shugabar Ofishin Kula da Basuka a Najeriya Patience Oniha ta ce duk gwamnatin da za ta gaji ta Shugaba Muhammadu Buhari a ƙarshen watan Mayu za ta tarar da bashin da ya kai kusan naira tiriliyan 77.
Ta bayyana haka ne ranar Laraba yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da kasafin kuɗin ƙasar na 2023, wanda gwamnatin za ta cike giɓinsa ta hanyar ciyo bashi.
Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta ce za a samu kashi 22 cikin 100 na kuɗin shigar da aka yi hasashe ta hanyar cinikin man fetur, yayin da za a samu kashi 77 daga wasu harkokin daban.
Don cike giɓin, ministar ta ce sai an karɓo bashin naira tiriliyan 7.04 a cikin ƙasar da kuma tiriliyan 1.76 daga ƙasashen waje. Haka nan za a karɓo tiriliyan 1.77 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma sayar da kadarorin gwamnati da za su samar da naira biliyan 206.
A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan kasafin kuɗin na 2023 kan sama da naira tiriliyan 20, wanda ke da giɓin tiriliyan 11.