Advertisements
Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana cewa akalla kuɗin da ake neman a CBN zuwa yanzu za su iya kai Tiriliyan 90. Ya bayyana haka ne a wata zantawa da Sashen DCL Hausa suka yi da shi a ranar Asabar 7 ga watan Janairu, 2023.
Kazaure yace kuɗin da ya ƙiyasta a kwanakin baya cewa Tiriliyan 85 yana maganar a shekarar 2020 ne, yace yanzu kuma ana maganar shekarar 2023, yace zuwa yanzu kuɗin za su iya kai Naira Tiriliyan 90.