Biyo bayan kai hari ‘yan Bindiga an rufe tashar jirgin Ƙasa a Edo

Advertisements

Hukumomi a Nijeriya sun bayyana cewa a kulle tashar jirgin Ƙasa ta Wajen da ke jihar Edo, bayan kai hari da akayi tare da awumgaba da mutanen da ba’asan addinai ba.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta
Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba.
To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan.
Ya ce ‘yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa, inda suka kwashe tsowon watanni a hannun ‘yan bindigar.
Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙasar dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin manyan biranen biyu na kusan sama da wata shida.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like