Advertisements
Wani matashi ɗan shekara 20, mai suna Gaddafi Sagir, ya kashe kishiyar mahaifiyarsa mai suna Rabi da kuma yar ta, Munawwara a jihar Kano.
Yana da kyau ka duba wannan👉 https://bit.ly/3ruFOdf
Lamarin ya faru ne a jiya Asabar da misalin ƙarfe 10 ma dare a unguwar Fadama da ke Rijiyar Zaki a jihar Kano.
Duba wannan 👉 https://bit.ly/3OerbEx
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matashin na zargin marigayiya Rabi da yin sanadiyyar rabuwa da mahaifinsa, shi ne ya buga mata ƙarfe a wuya da goshi, nan take ta faɗi ta rasu da tsohon ciki a jikin ta
Advertisements
Ka karanta wannan kuwa 👉 https://bit.ly/3OjYt59
Rundunar ƴan sanda a Kano, ta bakin kakakin ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka rundunar ta kama wanda ake zargin, inda ya ce a yayin binciken farko, ya amsa cewa shi ne ya kashe mamatan.
Ƙarin bayani na nan tafe…