Advertisements
Yadda Kamfen Shugaban Kasa Ke Gudana Yau a Damaturu Talata, Janairu 10, 2023 at 3:48 Yamma daga AbdulRahman Rashida Ba tare dabata lokaci ba daga jihar Adamawa, Jirgin shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan jiga-jigai kuma mambobin kwamitin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress APC ya garzaya jihar Yobe.
Shugaba Muhammadu Buhari, tare da dimbin hadimansa zasu tafi kaddamar da kanfen Tinubu a jihar tare da neman zarcewa Mai Mala Buni. 3:39 Yamma Ku yi noma, Buhari ya yi kira ga al’ummar Yobe Shugaba Buhari yace: “Ba abinda zan fadi da ba’a fadi ba. Abinda ya kawo ni nan Yobe daga Adamawa shine jam’iyyarmu ta APC ta yarda da cewa Ahmed Bola Tinubu shine wanda jam’iyya ta tsaida … saboda haka abinda ya kawo ni kenan.”
“Tun da karfe 12 ko kafin lokacin kuke cikin rana kuka saurari yadda muka samu kasa shekara bakwai da suka wuce.” “Kun fi kowa sanin cin mutuncin da Boko haram sukayi muku, suka kona makarantu, suka hana yaranku karatu, saboda haka Allah ya taimakemu mun ga bayansu.”
“Ina son ku maida hankali idan Allah ya kawo damina ku noma abinda zaku ci. Idan damina ta wuce ku smau sana’ar da zaku yi.” “Ni na tashi maraya, ban san mahaifi na ba. Kuyi iyakan kokarinku ku biya amanar da aka baku da ta iyalin ku.”
“Abin duniya abin banza, ku rike amana, ku rike jama’ar da ke karkashin ku.” “Na shekara 80, na yi aikin soja, na yi na ofis, na shiga siyasa, na nemi shugaban kasa sau uku, na shiga shari’a na ce a tausaya min, sai aka min dariya” “Dan Allah ku zabi wanda kuke so. Ku kun sani iyakan kokarin da mukayi.
Zamu cigaba da aiyukan kokarinmu, Zamu tabbatar da cewa an zanna lafiya, ya kiyayemu daga dukkan sharri.” “Mu mun gama namu Insha’aLLahu, nan da wata biyar zamu koma gida.”