Wata sabuwa: Ba matsalar tsaro ne ya damu Najeriya ba – Zakzaky

Advertisements

NI BAN YARDA TSARO NE MATSALAR KASAR NAN BA_ Inji Sheikh Zakzaky 
Jagoran Yan Shi’a Wato Sheikh Zakzaky Yace Shi Be Yarda Cewa Tsaro ne Matsalar Nigeria Ba.
Yace Ni ban yarda  cewa tsaro ne matsalar mu a kasar nan ba Abinda ke damun mu a kasar nan, ainihin rashin asasin da Muka doru  a kaine da rashin sanin Ina muka dosa. Shi rashin tsaron nan , su mahukuntan suke haddasawa.
Ba wani Wanda ya kawo rashin tsaro a kasar nan, in banda su. Ma’ana wato shi rashin tsaron makamin siyasa ne. Don zamu ga cewa; ainihin ma an zabi a ina ne za’a samar da tsaro din, Ina ne Kuma (su wa za’a tsoratar). 
Alal misali munga da gangan an zabi cewa da arewacin kasar nan za’a yi , Kuma ma da musulmi. Kuma idan ka duba za ka ga matsaloli suna nan  a ko’ina a kasar nan.
Amma kuma mun tabbatar da cewa; matsalolin da suke jingina ma arewacin kasar nan, ala’amarin ba haka ba ne. Don mun San Lallai in ana batun tarbiyya ne , mu mun fi su ma tarbiyya, Amma sai su kawo rashin da’a ya fi yawa a wurinmu.
Saboda haka , ka ga ya Zama abin, makamin siyasa ne , ya zama wasa  ne ‘yan siyasa suke yi da rayuka da dukiyoyin mutane. 
Daga Bin Muhammad KD
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like