Likitoci 7 sun rasa ransu sa kamakon cutar Ebola a Ƙasar Uganda – WHO

Advertisements

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana kasar Uganda a matsayin wacce ta rabu da cutar Ebola, kwanaki 42 tun bayan samun mutum na karshe da ya kamu da cutar.

SHIGA NAN DOMIN SAMUN LABARANMU NA YAU DA KULLUM 👉 https://bit.ly/3IEq8gQ

An bayyana hakan ne a wani taro a gundumar Mubende, wadda a yanzu aka fi sani da cibiyar barkewar cutar Ebola nau’in Sudan karo na biyar a kasar Uganda.

Barkewar kwayar cutar nau’in Sudan, wadda aka fara gani a watan Satumban 2022, ya yi sanadin mutuwar mutane 55.

Dr. Jane Ruth Aceng, Ministar lafiya ta Uganda, ta ce manyan abubuwan da ke haifar da yada cutar su ne kamuwa da cutar a cikin gida da kuma taruka a wurare masu zaman kansu.

Advertisements

A ranar Laraba aka cika kwanaki 113 da fara barkewar cutar Ebola da kuma kwanaki 42 da sallamar mutum na karshe da aka tabbatar ya kamu da cutar, labarin da kasar ta dade tana jira.

Aceng ta ce “Yanzu na tabbatar cewa an dakile dukkan hanyoyin yada cutar. Kuma zan yi amfani da wannan damar wajen shelar cewa an kawo karshen barkewar cutar kuma yanzu Uganda ba ta da cutar Ebola.”

Gundumar Mubende ta yi rajistar adadi mafi yawa inda ta sanar da samun mutun 64 da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma mace-mace 29.

Yayin da jami’an lafiya 7 ke mutuwa sakamakon cutar Ebola, jami’ai da yawa na jin tsoron tunkarar masu fama da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *