Saboda kaunar Buhari har fasaman hannu aka yi da Bindiga – Inji Gudaji Kazaure

Advertisements

Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana yadda suka sha artabo da jami’an tsaro har suka kai ga sun harbeshi da Bindiga ya saboda kaunar da yake yiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne a ya yin zantawarsa da sahen DCL Hausa a ranar Talata.
Ya bayyana cewa akwai wani lokaci da ya sayi manyan riguna guda biyu ya zo zai kaiwa Shugaban Kasa Buhari wata rana a Kaduna, yana zuwa sai ya iske ya kwanta, sai Security nasa yace maigida ya kwanta.
Bayan ya juyo zai koma gida sai ya haɗu da wasu mutane da kayan sojoji suka tare shi, inda suka tambaye sa kudi ya basu, suke nemi kwace masa kayan da zai kaiwa Shugaban Kasa Buhari ya hana, a nan ne suka harbeshi.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like