Wani Matashi ya cinna wa kansa Uta bayan ya kashe budurwarsa kan zarjin cin amana

Advertisements

Wani saurayi mai suna Babe Face ya kashe budurwarsa tare da ƙona kansa ƙurmus a garin Kom Kom na karamar hukumar Oyigbo da ke jihar Fatakwal.
Wani ganau ya bayyana cewa saurayin ne ya gayyaci budurwarta sa zuwa gidansu a karshen mako, inda nan take rikici ya shiga tsakaninsu lokacin da saurayin ya zargi marigayiyar da cin amanarsa.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shaidan ya ce lokacin da budurwar ta kasa yi masa bayani kan zarginta da yake yi, kawai ya hau kanta da duka wanda kuma shi ya kai ga rasa ranta.
Har ila yau, shaidan ya ƙara da cewa bayan kashe budurwar a kokarinsa na ɓoye abin da ya aikata, nan take saurayin ya cinnawa dakin wuta tare da ƙona kansa da kuma gawar budurwarsa.
Ganau din ya kuma ce lamarin ya janyo fargaba a zukatan mutanen yankin, inda da dama daga ciki suka tsere tare da barin yankin saboda tsoron kada jami’an tsaro su kama su.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin ‘yan sandan jihar ta Fatakwal, SP Grace Iringe Koko, ta ce bata da labarin abin da ya faru kawo yanzu.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like