YANZU-YANZU: Batun ƙara kuɗin Datar Yanargizo ya ƙoƙarin jefa Ƙasar Nijer cikin wani hali

Advertisements

A jamhuriyar Nijer matakin karin kudin datar internet ya haifar da damuwa a wajen jama’a musamman masu amfani da yanar gizo wajen gudanar da harakokinsu na yau da kullum.
NIAMEY, NIGER — 
Dalilin haka ne suka yi kiran kamfanonin wayar tafi da gidanka da hukumar zuba ido a kan sha’anin wayar sadarwa su dubi wannan lamari da idon rahama.
Kamar yadda kamfanonin wayar sadarwa suka sanar ta hanyar sakon text din da suka aike wa masu amfanin da layin wayar tafi da gidanka a farkon watan nan na Janairu sabon farashin datar internet ya fara aiki a ranar Lahadi 15 ga watan da muke ciki inda aka lura da karin kashi 50 zuwa 70 daga cikin 100 matakin da ya jefa dimbin mutane cikin halin zullumi.
Wasu mazauna birnin Yamai sun yiwa Muryar Amurka bayani a kan wannan lamari.
Shugaban kungiyar RAP DAP ta matasa masu aiki da yanar gizo-gizo Awal Oumarou Ibrahim na da damuwa akan koma bayan da matakin zai haddasa wa harakokin matasa.
Kusan komai na sha’anin karatu a yau musmman a jami’oi kan gudana ne ta hanyar internet dalili kenan dalibai ke korafi da karin kudin data.
Kamfanonin wayar sadarwa a sakon text din da suka tura wa jama’a sun danganta karin farashin da abinda suka kira sabuwar dokar kayyade kudin internet da hukumar zuba ido akan sha’anin yanar gizo wato ARCEP ta kafa, to sai dai wani jami’inta Malan Tahirou Massaoudou ya nisantar da hukumar ta ARCEP da hannu a wannan lamari.
Ya na mai cewa dokar 2018 ta bai wa kamfanonin wayar sadarwa cikeken ‘yancin kayyade farashi saboda haka babu hannun ARCEP a wannan kari.
Abinda ya faru shine bincike ne da muka gudanar ya ba mu damar gano cewa kamfanonin waya na yawaita fakewa da tsarin Bonus da nufin kiran kasuwa, to sai dai a yadda abin ya tsananta ba za iya fayyace zahirin wainar da kamfanonin ke toyawa ba ballantana a san girman cinikin da suke samu sannan ba a san nawa ake tatsar masu amfani da waya ba idan aka ba su bonus, shi yasa muka bukaci su koma kan hanya amma babu inda ARCEP ta umurcesu su tsauwala farashi.
Ganin yadda jama’a ta fusata akan wannan batu har wasu kungiyoyi suka fara kira a kauracewa sayen data ya sa shugabanin hukumar ARCEP da na kamfanonin wayar sadarwa suka gudanar da taron gaggawa a jranar Litinin inda a karshe suka sanar cewa sun fahimci juna a bisa sharadin kowane kamfani ya sake duba tsarin farashin da ya bullo da shi .
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *