YANZU-YANZU: Abubuwa har guda goma da ake zargin Abba Kyari ya aikata su

Advertisements

Akinrinbosun ya ce an yi masa tayin naira miliyan 10 domin ya ce Saraki ya bukaci su gudanar da wannan aikin na fashi da makami.
Daya daga cikin manyan wadanda ake tuhuma a shari’ar fashin bankin Offa a wata babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin, Mista Ayoade Akinrinbosun, a jiya, ya shaida wa kotun yadda tsohon kwamandan rundunar IRT, Abba Kyari ya ba shi Naira miliyan 10. domin tuhumi tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, a shari’ar fashi da makami.
Ya kuma shaida wa kotun cewa Kyari ya yi alkawarin ba shi takardar bizar kasar da ya ga dama idan ya goyi bayan matakin da ake na tuhumar Saraki, amma ya ki amincewa.
‘Yan sanda sun gurfanar da wasu mutane biyar, Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham da wasu mutane biyu a gaban kotu bisa laifin hada baki na fashi a bankuna, kashe ‘yan sanda tara da wasu ‘yan kasar, da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Yayin da lamarin ya faru, kimanin mutane 10 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu mazauna garin Offa suka samu raunuka.
Sai dai a yayin da lauyan masu kare Mista Mathias Emeribe, SAN ya yi masa tambayoyi, Akinrinbosun ya ce an yi masa tayin naira miliyan 10 domin ya ce Saraki ya bukaci su gudanar da wannan aikin na fashi da makami.
A cewarsa,” shi (Abba Kyari) ya ce ya kamata in yarda kuma in ce Saraki ne ya ce mu je mu yi fashi. Na ce masa ba zan yi haka ba. Da na gwammace in mutu saboda abin da ban yi ba, da in yi ƙarya ga marar laifi. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta rawaito a ranar 19/1/2023
_ATP HAUSA
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like