Zaɓen 2023: Yadda Ƙungiyar Izala ta yi Na’am tare da karɓar tawagan Atiku a jami’ar Assalam (AGUH)

Advertisements

✍️ Ibrahim Baba Suleiman 
Kungiyar wa’azin musulunci ta jama’atu Izalatil Bid’ah wa iqamatis sunnah, Mai kira da ayi addini kamar yadda Annabi mai tsira da aminci su tabbata a gare shi yayi, kuma a kau da kirkirarrun abubuwa a cikin addini, ta karbi tawagar wakilan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP maigirma wazirin Adamawa, Alh. Atiku Abubakar, a jami’ar ta “Assalam Global University” (AGUH) mallakar Izala dake birnin Hadejia a jihar Jigawa.
Tawagar ta maigirma wazirin Adamawa karkashin jagorancin tsohon ministan gona a Naijeriya Alh. Sani Zangon Daura, ta hada da, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alh. Attahiru Dalhatu Bafarawa, Garkuwan Sokoto, tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sen. Adamu Aleiru, Dr. Usman Bugaje, Alh. Kwairanga Jada, Dr. Jameel Muhammad Sadis, Dr Ibrahim Usman Yakasai, Alh. Ibrahim Little, Alh. Abubakar Shehu, Alh. Dahiru Bobbo da tsohon sakataren Izala Alhaji Yaya Abubakar Aga.
Tun farko, a cewarsa, tsohon minista Alh. Sani Zangon daura yace sunzo garin hadejia ne, bisa wakilcin Alhaji Atiku Abubakar (wazirin Adamawa) domin domin ganin yadda aikin wannan jami’ah ke gudana da kuma yadda shima zai sanya tashi gudummawa wajen wannan aiki na jami’ah ta wannan kungiya mai tarin albarka.
Tawagar wanda ta samu  tarba daga manyan wakilan Kungiya ta kasa Karkashin Jagorancin Daraktan Agaji Engr. Mustapha Imam sitti, da Mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Garba Goje, daraktan gine-gine na kungiyar, Engr. Ashiru Babandede, Sakataren ilimi na kwamitin ilimi, Dr. Ibrahim Abdullahi R/lemo, shugaban JIBWIS na jihar Gombe, kuma sakataren ayyuka a majalisar agaji ta kasa, Engr. Salisu Muhammad Gombe, shugaban JIBWIS social media na kasa, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman da sauran shugabannin Jibwis na kasa da kuma na jihar Jigawa baki dayansu.
Tun farko Imam Sitti, ya gabatar musu da jawabin maraba da kuma gabatar da ‘yan tawagar dake tare dashi.
Shi kuma darakta furojet Engr. Ashiru Babandede, ya zaga kusan dukkan jami’ar da bakin, inda ya musu cikakken Bayani inda aka kwana da inda za’a tashi. Tawagar ta dauki alkawarin gina wasu gine-ginen a cikin jami’ar insha Allah.
JIBWIS NIGERIA
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like