Nijeriya ta kashe biliyoyin kuɗi waje sayan makamai domin yaƙar ‘yan ta’adda

Advertisements

Murtaniya – Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta kashe sama da dala biliyan daya wajen siyo kayan aikin yakar boko haram a yankin arewa maso gabas.
Shugaba Buhari yace: “Lokacin da na karbi mulkin Nigeria a shekarar 2015, yan kungiyar Boko Haram sun kusan mamaye daya bisa uku na jihar Barno, da wasu bangarori na jihar Yobe da kuma wasu kananan hukumomim mulki da suke hannunsu”
Shugaba Buhari na wannan jawabin ne a wajen taron zaman lafiya na kasashen Africa da ake gudanarwa a Murtani.
Buhari ya ci gaba da cewa mun samu damar kwato wadannan garuruwan da kuma wasu gurabe da suka kwace. Shugaba Buhari yace mun samu damar zuba zunzurutun kudi sama da dala biliyan daya wajen samar da makamai da kayan aikin da za’a yaki wadannan yan ta’addan tun daga 2015 har zuwa yanzu.
Channels Tv ta rawaito ta samu kwafin wannan takardar da mai magana da yawun shugaba kasa ya sanyawa hannu da take cewa shugaba Buhari zai ci gaba da hada karfi da karfe da sauran kasashen da suke makotantaka da su wajen ganin an kawo karshen matsalar a yayin taron dai an karrama shugaba Buhari da lambar girmama ta Abu Dhabi dan himmarsa wajen bukasa zaman lafiya a Nigeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari yace ya kamata ace zama ko taron da za’ai na gaba, kasashen Africa suyi duba na tsanaki kan abubuwan da suke faruwa a kasar Libya da kuma samar musu da mafaka.
Shugaba Buhari yace: “Akwai san rai da kuma san zuciya ga wasu kasashe da suke nunawa kan kasar Libya, wanda shine dalilin kin kawo karshe tashin tashinan nan” “Indai ana so ai maganin wannan matsalar to dole ne a dubi kasar sannan asan abun da ya kamata ayi akanta”
Shugaba Buhari ya kara nanata kudirin gwamnatinsa wajen bada hadin kai dan ganin an samu kulla alaka a tsakaninsa da kasashen African wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakaninsu.
 Shugaban kuma ya roki sauran shugabannin kasashen Africa da suka halarci taron da su aiwatar da abinda suka koya ko aka basu shawara kan zaman lafiya ko kuma daga sauararon bayannan da shugaban kasashen sukai. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like