Saudiyya ta yanke wa wani Malami hukuncin kisa saboda yana amfani da Whatsapp da Twitter

Advertisements

BABBAR MAGANA: An yanke wa wani babban Malami hukuncin kisa saboda yana amfani da Whatsapp da Twitter
Kasar Saudiyya ta yanke wa wani babban Malamin Addinin Musulunci, kuma Lakcara a Jami’a hukuncin kisa, saboda yana amfani da Whatsapp da Twitter wajen sukar Gwamnati.
Babban Malamin mai suna Awad Al-Qarni. Malamin ya koyar a King Khalid University da ke Saudiyya, kuma yana fitowa a gidajen Talabijin ana ganawa da shi.
Rahotannin sun nuna cewa a shekarar 2017 ya taɓa sukar Gwamnatin Saudiyya kan hukuncin da ta yanke wa wasu yan kungiyar yan Burazas. 
Hakazalika yanzu ma ana zarginsa da sukar Gwamnatin Saudiyya a Manhajar Whatsapp da Twitter kan al-mundahana da kuɗaɗen kasar wajen shigowa da yan kungiyar kwallon kafa. Me zaku ce?
Daga Usman Umar Katsina
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like