Wani Ɗalibi a Jami’ar Fasaha ta Akure da ke jihar Ondo ya rataye kansa

Advertisements

Wani dalibi mai mataki 300 na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure, Olona Oluwapelumi, ya kashe kansa a gidansa da ke Unguwar Aule a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Marigayin wanda aka fi sani da Black, an ce yana Sashen Zane-zanen Masana’antu a Jami’ar. An ce ya rataye kansa a dakinsa.
Ba a san dalilan da ya sa ya dauki matakin a kansa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Wata majiya a makarantar ta bayyana cewa a ranar Asabar ne abokan marigayin suka je dakinsa suka gano a kulle, bayan da aka yi ta kiraye-kirayen da ba a amsa ba, sai aka karye kofar, aka same shi a rataye.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like