YANZU-YANZU: Kamfanin Google ta na shirin korar mutum a ƙalla 12,000 a faɗin duniya

Advertisements

Kamfanin Alphabet masu mallakin kamfanin fasaha na Google ya bayyana cewa zai rage ma’aikata 12,000 a faɗin duniya, yana mai bayyana matsin tattalin arziki a matsayin abin da ya tilasta wa kamfanin fasahar sake sauya fasalinsa.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin Microsoft ya ce zai rage yawan ma’aikatansa zuwa 10,000 a cikin watanni masu zuwa, bayan da kamfanonin Facebook da Amazon da Twitter suka bayyana makamancin wannan matakin.
Rage ma’aikatan da kamfanonin fasaha ke yi na zuwa ne bayan da a baya kamfanonin suka ɗauki ma’aikata masu tarin yawa a lokacin annobar corona kokacin da mutane suka koma aiki da karatu daga gida ta hanyar intanet.
“A cikin fiye da shekara biyu mun samu gagarumar ci gaba”, kamar yadda shugaban kamfanin na Alphabet Sundar Pichai ya shaida wa ma’aikatan kamfanin a wani saƙon email da ya tura musu.
Kamfanin na da kusan ma’aikata 187,000 a faɗin duniya zuwa ƙarshen watan Satumban 2022.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *