Advertisements
Asusun Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya yi alkwarin ci gaba da tallafawa bangaren ilimi a arewa maso gabas ta yadda yara da yawa za su samu damar zuwa makaranta.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms Christian Munduate, ce ta bayyana hakan lokacin da ta kai ziyara Jami’ar AUN da ke Yola a ranar Litinin don gudanar da shirin tallafawa yara 100 da basa zuwa makaranta da abinci da kuma abubuwnan karatu.
Ta bayyana kokari da suke na ganin ƙarin yara sun samu damar karatu ta Jami’ar da kuma sauran makarantu a faɗin yankin.
Munduate ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su bijiro da shirye-shirye da za su kawo ci gaban ilimi a kananan matakai, inda ta nuna bukatar ganin hobbasar bangarori masu zaman kansu saboda ci gaban ilimin yara ƙanana.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Ms Christian ta ce akwai bukatar bai wa yara ilimi saboda idan ba a basu ba, za su iya zama kalubale a nan gaba.
Wakiliyar ta UNICEF ta shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su ci gaba da zuwa makaranta domin samun ilimi saboda zai zamanto mai amfani a garesu da iyalansu da kuma al’umma.