Advertisements
Malam Daurawa ya bayyana yadda Musulmai suka tsani Turawa da yadda suke kyamarsu.
Ya bude wani sirri, ya ce Turawa sun fi Larabawa kaunar bakaken fata ‘yan Afrika.
Ya ce abin mamaki ne yadda ake kin Turawa amma ake son Larabawa kai tsaye.
Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya ya bayyana cewa, Turawa sun fi son bakaken fata fiye da yadda Larabawa ke kaunarsu.
Ya kuma bayyana cewa, bakaken fata na son Larabawa, amma basu fiye son bakar fata ba sai dai idan ya iya Turanci ko kwallon kafa.
A cewarsa, Turawa suna kashe kudi kan dan Afrika saboda kauna, amma duk da haka kallon sharri ake yi masa a wannan nahiyar.
Najeriya – Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, alamu masu karfi sun nuna Turawa sun fi son bakaken fata fiye da Larabawa. Daurawa ya ce, bakaken fata Musulmai na kaunar Larabawa, amma kwata-kwata su Labarawan ba wani son bakake suke ba.
A cewarsa, Larabawa sun fi nuna sha’awa da kaunar Turawa, yayin da su kuma Turawan ke tsoro da gyamar Larabawa a cikinsu.
Daurawa ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyon da aka yada a kafar Facebook, inda yake bayyana alaka tsakanin duniyar bakin fata Musulmi, Bature da Balarabe.