YANZU-YANZU: Gwamna El-Rufai ya yi ƙira ga CBN kan daina ƙarɓar tsoffin kuɗi

Advertisements

Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin CBN da ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudi.
Gwamnan na jihar Kaduna ya ce mutanen karkara ne wa’adin CBN zai fi yi wa illa.
Ya ce yawancin garuruwan karkara basu da bankuna balle har su kai kudadensu.
Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci babban bankin kasa da ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudade a kasar.
El-Rufai ya ce wannan mataki na CBN zai fi shafar al’ummar karkara ne saboda yawancinsu basu da bankuna.
Da wannan ne gwamnan ya yi kira ga babban bankin Najeriya da ta kara wa’adin daina karbar kudaden.
Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudi cewa lokacin ya yi gajarta da yawa, rahoton Channels TV.
 Babban bankin Najeriya dai ya ce za a daina amfani da tsoffin kudade a kasar daga ranar 31 ga watan Janairu lamarin da ya jefa al’umma musamman talakawa a halin wayyo Allah.
El-Rufai ya bayyana cewa mutanen karkara da dama wadanda basu da hanyar yin hada-hada kudi sune wadanda wannan hukunci zai fi shafa.
Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna, gwamnan ya nanata cewa babu ta yadda za a yi manoman karkara da yan kasuwa a yawancin garuruwan jihar su cika wa’adin CBN na kai tsoffin kudinsu banki. Ya bayyana cewa wasu kananan hukumomin basu da kowani banki a cikinsu, don haka ba a sako su cikin wannan tsari ba kenan.
Yayin da yake nuna goyon bayansa ga sauya kudin da CBN ya yi, El-Rufai ya bayyana cewa ya zama dole a baiwa mutanen yankunan karkara karin dama da za su sauya tsoffin kudadensu duk da cewar da ya yi damar da suke da shi dan kadan ne.
Saboda wannan, gwamnan ya yi kira ga CBN da sauran bankuna da su samar da hanyoyin sauya tsoffin kudaden a garuruwan karkara.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like