Kamfen: Gwamnan jihar Bauchi ya zo da sabon al’amari

Advertisements

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yace gwamnatin sa na buƙatar ƙarin wa’adi don kammala ayyukan ta na ciyar da al’uma gaba da suka haɗa da inganta kasuwanci don farfaɗo da tattalin arziki.
Bala Muhammad na jawabi ne yayin rangadin neman goyon baya a ƙaramar hukumar Ganjuwa inda ya ziyarci iyayen ƙasa, masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umar yankin.
A cewar gwamnan Allah ya azurta Ganjuwa da faɗin ƙasa da harkokin kasuwanci inda yace gwamnatin sa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da manyan ayyukan ta a yankin sun kammala domin sauƙaƙa rayuwar manoma da mazauna yankunan karkara.
Yace gwamnatin sa na duba yiwuwar faɗaɗa kasuwar Soro wacce tayi fice a Arewa a wani matakin haɓaka kasuwanci da samar da ƙarin kuɗaɗen shiga.
Gwamna Bala yayi kakkausan suka kan salon shugabancin sanata me wakiltar Bauchi ta tsakiya wanda ɗa ne a ƙaramar hukumar inda yace yayi watsi da buƙatun da al’umar sa ke da su.
Yace idan aka zaɓa masa ƴan majalisun jiha, wakilai da na dattawa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP za’a ga sauyi musamman wajen samar da romon dimokraɗiyya da kowa zai yi alfahari da shi.
Da yake yabawa hakimai, sarakuna, dagatai da masu littafin ƙasar Ganjuwa Bala Muhammad yace a matsayin sa na ɗan su zai cigaba da daɗaɗa musu tare da tallafawa wajen sauƙe nauyin shugabancin da suka gada iyaye da kakanni.
Ya ƙara da cewa manyan ayyukan da gwamnatin sa ta samu nasarar kammalawa sun haɗa da manyan titunan da suka gagari gwamnatocin baya, kwaskwarima wa fadoji da sakatariyar ƙaramar hukuma da makaranti a saboda haka yace zai ruɓanya ninkin su a zango na biyu.
A jawaban su daban daban shugabannin yankunan da gwamnan ya ziyarta sun bayyana farin ciki da godiyar su kan ayyukan da kuma ziyarar tare da jaddada goyon bayan su a gare shinda ɗaukacin ƴan takarar jam’iyyar PDP da suka ce ta bar abin nunawa masu tasowa.
Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani
Janairu 27, 2023.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like