Gyaran Tako: An baza Jami’an tsaro a birnin Kano gabanin zuwa Shugaba Buhari

Advertisements

Rahotanni sun nuna cewa an tsaurara jami’an tsaro a ƙwaryar birnin Kano domin tarbar Shugaba Muhammadu Buhari.
Manyan hanyoyi musamman waɗanda ake sa rai zai bi cike suke da jami’an tsaro ta ko ina.
Shugaban zai zo Kano ne domin buɗe wasu muhimman ayyuka da ya yiwa jihar.
Jihar Kano dai jiha ce da Shugaba Buhari ke da magoya baya da dama, kuma jiha ce da ya jima yana lashe ta a zaɓe.
Kafin wannan rana dai Gwamnatin Kano ta nemi ya dakatar da zuwan nasa amma bai amince da buƙatar hakan ba.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like