Karin bayani kan jifar da aka yi wa tawagar Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Kano

Advertisements

1- Hoto na farko shine jirgin Helicopter mai lamba 5N – FG2 da shugaba Muhammadu Buhari ya sauka dashi a Kano domin bude ayyukansa dana Gwabnatin Kano a yau. 
2. Hoto na biyu kuma shine jirgi kirar Helicopter da wasu marasa tsoron Allah kan abun da za’a tambaye su a ranar al’kiyama, suke yadawa wannan Hoto tare da cewa a yau an jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari harma an fasa masa jirgin sa. 
Wanda ko a kirar jirgin basu zama kala daya bama balle ace, kuma idan kana musu kayi amfani da goggles don samun cikakken bayanin yadda wannan photo ya samo asali a yanar gizo.
Allah ka yarda mu fadi gaskiya koda akan wanda bama so ne.
– Shu’aib Kabir
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like