YANZU-YANZU: Hukumar Kiwon Lafiya a Nijeriya sun fitar da sanarwar ta gaugawa

Advertisements

Ƙungiya Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya ta soke yajin aikin da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar.
Matakin na zuwa ne bayan ganawar da kwamitin zartarwa na ƙungiyar ya gudanar a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda ƙungiyar ta sake duba batun.
A cikin watan Janairu ne dai ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki a fadin ƙasar saboda kasa biya mata buƙatunta da gwamnati ta yi.
Likitocin dai na buƙatar a sake duba tare da inganta kuɗaɗen alawus ɗin horaswa da ake ba su, yayin da suke kuka da rashin biyansu wasu alawus-alawus, da rashin biyan wasu daga cikin mambobinsu da sabon tsarin albashi da ƙasar ta amince da shi.
Rahotonni sun ce a ƙarshen ganawar majalisar zartarwar ƙungiyar, likitocin sun yaba wa gwamnatin tarayya game da sakin sabuwar sanarwar biyan kuɗaɗen alawus-alawus na horaswa ga likitocin.
Haka kuma likitocin sun nemi gwamnatin tarayyar da ta biya wasu daga cikin mambobinta da ke bin gwamnatin bashin kuɗaden alawus-alawus
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like