TIRKASHI: Zan iya Rantsewa da Al-Qur’ani Buhari bashi da Kuɗin da ya kai Naira Biliyan Ɗaya – Alhaji Musa Haro

Advertisements

Idan Aka Ba Ni Al-Qur’ani Maigirma, Zan Iya Rantsuwa, Idan Shugaba Buhari Na Da Zunzurutun Kuɗi Naira Biliyan Ɗaya Ta Shi Ta Kansa Qur’ani Ya Ci Ni,  Cewar Alhaji Musa Haro
Ɗanmadamin Daura, hakimin Dumurƙul kuma daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Haro ya ce wallahi tallahi, na san da zan mutu ayi man hisabi ranar gobe lahira kuma idan aka ba ni Al-Qur’ani Mai Girma, zan iya rantsuwa da shi, idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari na da zunzurutun ƙuɗi da suka kai Naira Miliyan dubu daya, Al-Qur’anin nan ya ci ni.
Hadimin Shugaban Ƙasa kuma daya daga cikin makusantan shugaba Buhari, Alhaji Musa Haro ya bayyana haka a wajen wani taron kara wa juna sani kan sabbin kafafen Sadarwa da Ƙungiyar Jakadun El-Marzuq suka shirya a dakin taro na hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin jihar Katsina, yau Litinin.
Hakimin Dumurƙul a masarautar Daura ta jihar Katsina, Alhaji Musa Haro ya kara da cewa wani ya je ya yi rubuta labarin karya a kaina, inda ya ce ni ɗin nan, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da mafi yawancin mutane suka fi sani, ya dauki Naira Biliyan daya ya ba ɗanmadamin Daura, ya raba mutane a lokacin Korona, ya raba shi da Sarkin Daura, sun cinye da kuma tirelar shinkafa hamsin.
Hadimin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya cigaba da cewa har shugaba Buhari ya zama shugaban kasa, ni ke kula da asusun bankinsa, inda ya ke ajiiye taro da sisinsa, ni na riƙe shi. Amma har wani ya rubuta ya ba ni Naira Miliyan dubu daya, ace ya ba Musa Haro, an dauko tirela hamsin ta shinkafa, na je Kano na saida arba’in, na zo Daura na raba goma, shi aikin alheri ba’a faɗin shi, idan an yi don Allah.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like