Zaɓen 2023: Tsadar man fetur zai kawo koma baya wajen Shirye-shiryen Zaɓe – INEC

Advertisements

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce matsalar ƙaramncin man fetur da ƙasar ke fuskanta ka iya shafar tsare-tsaren hukumar game da za ta shirya zaɓen ƙasar da ke tafe.
Shugaban Hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a lokacin taron tuntuɓa tsakanin hukumar da ƙungiyoyin direbobin haya na ƙasar waɗanda suka haɗar da NARTO da NURTW da sauransu.
“Hukumar zaɓe tana tare da ku game da kokenku na ƙarancin man fetur da ƙasar nan ke fuskanta, da yadda hakan zai shafi hakar sufuri musamman a ranar zaɓe,” in ji Mahmood.
Ya ƙara da cewa “magana ta gaskiya ita ce rashin wadataccen man zai shafi shirye-shiryenmu”.
Shugaban hukumar ya ce dangane da wannan dalili , hukumar zaɓe za ta gana da kamfanin mai na ƙasa NNPCL domin duba hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance wannan matsala.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like