Advertisements
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar Sa Kai 41 biyo bayan wata arangama da suka yi da ɓarayin daji a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Kakakin rundunar SB Gambo Isah ya bayyanawa manema labarai haka a Katsina acikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin ranar juma’a.