Advertisements
An kama wasu ‘yan kasar waje mazauna Najeriya da suka mallaki katin zabe yayin da zabe ke karatowa An kwato katukan zabe 106 a jihar Kwara.
Hukumar shige da fice ta yi karin haske game da halin da ake ciki Saura kwanakin kadan a yi babban zaben 2023, an gargadi ‘yan kasar waje su guji yin zaben a Najeriya.
Ilorin, jihar Kwara – Hukumar kula shige da fice ta Najeriya (NIS) ta kama katukan zabe na PVC guda 106 a hannun wasu ‘yan kasar waje a jihar Kwara, TheCable ta ruwaito.
Aminu Shamsuddin, kwamtulan NIS a jihar ne ya bayyana hakan a ranar Litinin 6 Faburairu, 2023, inda yace an kama ‘yan kasar wajen ne a yayin sintirin da jami’an hukumar ke yi a birnin Ilorin na jihar.
A lokacin wani shirin wayar da kan, ‘yan kasar waje sun tsorata da jin cewa duk wanda aka kama shi ya kusanci zaben Najeriya zai sha dauri, a maida shi kasarsu kana a sanya shi a bakin jadawali.
“Wasu daga cikin ‘yan kasar wajen da ke da katin zaben Najeriya da kansu suka ajiye katukan kuma suka koma kasashensu, za su dawo bayan kammala zaben.