Shugaba Buhari ya sauke Shugaban asusun Inshora NSITF daga Kujerarsa kan wasu dalilai

Advertisements

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauke shugaban asusun Inshora na Najeriya (NSITF), Michael Akabogu.
 Wani ma’aikaci a NSITF ya tabbatar da an sauke shugaban domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa na bogin shaidar NYSC.
 Rundunar ‘yan sanda na bincike kan takardar da yake amfani da ita ta gama bautar ƙasa kuma NYSC ta ce Satifiket din ba nata bane.
Abuja – Bayanai sun nuna cewa an sallami babban Daraktan Asusun Inshora na ƙasa (NSITF), Mista Michael Akabogu, daga aikinsa.
 Har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka kori dataktan NSITF daga aiki amma wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa matakin ba zai rasa alaƙa da zargin bogin takardar shaidar bautar ƙasa (NYSC) da ake masa ba.
Wata majiya mai karfi a NSITF, wacce ta tabbatar da lamarin ga jaridar Daily Trust, ta ce an umarci ya sauka daga kujerarsa ne kafin gama bincike da ‘yan sanda suke a kansa.
Yayin da aka nemi jami’ar hulɗa da jama’a ta NSITF, Misis Ijeoma Oji-Okoronkwo, ba’a same ta ba har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton, wayarta a kashe. 
Jaridar Leadership ta tattaro cewa hukumar ‘yan sanda ta gayyaci shugaban NSITF, mai mallakin takardar shaidar gama aikin bautar ƙasa A030544 bayan shigar da ƙorafi a kansa.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like