Advertisements
Daga: Mujaheed Umar D Giwa
“Bani bukatar na ɗauki wani lokaci ina mana bayani yadda ƙasa (Nijeriya) ta kasance. kowa ya sani. Ko sai nace muku ga halin da take ciki?
Sai nace muku ba amana? ba aminci a kan hanyoyi, ba shi a gidaje ba shi a sararin samaniya? sai na faɗa muku cewa babu ruwan Fanfo, ba man fetur, ba wutar lantarki? ko sai na faɗa muku babu ramuka a kan hanya? ko sai nace muku a na fama da rashin aikin yi? ko sai nace muku ɗabi’u sun lalace? duk kunsan wannan kowa naji a jika!
Ko sai nace muku makarantu ba komai, sun zamo gidajen ƙadangaru? ko sai nace muku asibitocin ƙasar nan sun zamo makasan, gidajen Kisa a kai ka a ƙarasa ka? In ana maganar matsalolin ƙasar nan kowa ya sani, kuma kowa yanaji a jika. Amma yanzu mene mafita?
Mafita ɗaya ce dawo wa addinin Allah Ta’ala ya zamo musulunci ke iko da tafiyar da kasar ba tsarin demokradiyya Bature ba.