Advertisements
ABIN KOYI: Wata Makarantar Haddar Kur’ani A Garin Zaria Ta Biyawa Yara Dalibai 30 Aikin Umrah
Daliban Makarantar haddar kur’ani ta NURUT TILAWAH INTERNATIONAL SCHOOL ZARIA suna kan gudanar da aikin Umrah a ƙasa Mai Tsarki bayan hukumar makarantar ta su ta biya musu kudin aikin.
Wasu daga cikon haziƙan Ɗaliban makarantar ne suka samu wannan dama ta zuwa Saudiyya don yin aikin Umrah.
Wannan za mu iya cewa tsari ne wanda ya kamata ya zama abin koyi ga sauran makarantu da suke da ikon yin makamancin haka. Saboda yin hakan zai dinga karfafawa yara dalibai gwiwa.
Daga Yusuf Yahaya Bamalli