DA ƊUMI-ƊUMI: Munyi nasarar kashe ‘yan Bindiga Huɗu da jikkata biyu a garin Jema

Advertisements

Da safiyar ranar Laraba an tashi da jin karar manyan bindigogi a garin Jema da ke cikin karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto wanda ya hada iyaka da Nijar, a cewar mazauna garin.

BIRNI N’KONNI, NIGER — 

Wasu mazauna garin da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana wa Muryar Amurka cewa sun fatattaki ‘yan bindigar da suka kashe mutane hudu tare da jikkata mutane biyu da ke kan hanyar zuwa kasuwar Illela, kamar yadda wani mazaunin Kalmalao ya bayyana.

Rundunonin tsaron wannan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai sun shaida wa wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako cewa basu da hurumin yin magana a radio a halin yanzu sai an kammala bincike da neman wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Advertisements

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu kafin babban zabe a Najeriya, lamarin da ya sa wasu ke tunanin ko zaben zai yiwu a yankin.

A wata hira da Mamane Bako yayi da wasu jami’ai da hukumar zaben INEC ta Najeriya ta bai wa horo a wannan yankin ikayar, da suka bukaci a sakaya sunansu, sun tabbatar da cewa idan har aka tura su yankunan da ke fama da matsalar tsaro ba za su je ba.

An dai yi jana’izar mutane hudu da ‘yan bindigar suka hallaka yayin da mutane biyun da ke rai hannun Allah ke asibitin Galmi a cikin gundumar Malbaza a Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like