Bai kamata Malamai su fake da Tiket ɗin Muslum-Muslum ba suna zaɓawa almajiransu ɗan takarar ba – Rigachukum

Advertisements

Babban Malamin Addinin Islama a Najeriya Sheikh Yusuf sambo Rigachukum yayi wankin Babban riga wa malamai masu fakewa da sunan musulim-musulim ticket, malamin ya ce wannan ba adalci bane isar da wata manufa ce kawai ta son rai.

Sheikh ya bayyana cewa yana goyon bayan ko wani malami ya fito ya wasa Dan takarar da yake so almijarnsa su zaba, amma ba wai a fake da sunan musulim-musulim ticket ba. Malamin ya ce ya kamata ayi koyi da salon mulki irin na su tafawa balewa da Sardauna. 

Advertisements

Kowa ya ajiye imaninsa a cikin zuciyarsa Ba wai a fake da musulim-musulim don biyan bukatar kai ba. Malamin ya bayyana haka ne a wani faifayin video da Ibrahim Ibrahim Yusuf Sambo ya wallafa a shafinsa na Facebook. Mai taimaka masa a kofofin sada zumuntar zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like