Advertisements
Yan Siyasa Na Son Shigo Da Ƴan Daba Domin Kawo Rikici Ranar Zaɓe.
Rundunar Ƴan Sandan Kano Litinin, Maris 06, 2023 at 2:05 Yamma daga Sharif Lawal Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tona wani yunkuri da wasu ɓata garin ƴan shiyasa ke shiryawa a jihar Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa akwai wasu ‘yan iskan gari dake son shigo da ƴan daba cikin jihar Sai dai rundunar ta bayyana cewa zamu yi iyakar yinmu ba tare da ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta hukunta duk wasu ɓata gari.
Jihar Kano- Rundunar ƴan sandan jihar Kano, a ranar Litinin ta fallasa wani shiri na wasu ɓata garin ƴan siyasa a jihar na son shigo da ƴan ɓata gari domin tayar da rikici a zaɓen gwamnoni dake tafe ranar Asabar. Rahoton Vanguard.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mamman Dauda, wanda wannan shirin a cikin wata sanarwa ta hannun kakakin rundunar ta jihar, SP Abdullahi Haruna, ya gargaɗi ƴan daba da masu neman tayar da fitina.
Da su ƙauracewa jihar ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri. Rahoton Tribune Haruna ya bayyana cewa rundunar zata haɗa hannu da sauran jami’an tsaro a jihar domin tabbatar da cafkewa da hukunta duk masu aikata wannan laifin.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta samu bayanin cewa wasu ɓata garin ƴan siyasa suna shirin shigo da ƴan daba cikin jihar da niyyar kawo hargitsi, “A zaɓen gwamna dana ƴan majalisar dokokin jiha na ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairun 2023.”