In baku zaɓi Uba Sani ba El-Zakzaky zai dawo Zariya – Gwamna El-Rufai

Advertisements

A yayin gabatar da wani taro da Gwamnan ya shiryawa Malamai ranar Alhamis 9/03/2023 a Congo dake cikin Zaria akan Malaman suyi Huɗuba akan wajibcin zaɓan Ɗan takarar gwamna na APC (Uba Sani) akan shine zai ɗora daga inda Nasiru El-Rufa’i ɗin ya tsaya.
 Gwamna El-Rufa’i ya yi Kakkausar suka ga Jagoran Harkar Musulunci A Najeriya wato Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) inda wasu daga cikin Malaman da suka halarci zaman suka shaida mana cewa gwamnan ya bayyana cewa: “Kunga dai yanda muka yi da El-Zakzaky da almajiran shi, mun wargaza komai nashi da Almajiran shi mun watsa su babu su. Yanzu Zakzaky da Almajiransa Zaria tafi ƙarfin su, don haka muka ce ku zaɓi Uba Sani don ya ƙarasa ruguza ‘yan ɗaiɗaikun da suka rage, in kuma kuka zaɓi wancan to zasu dawo Zaria.” – Inji El-Rufa’in.
Yayi maganganu sosai akan Ta’addancin da suka yi a Zaria da sunan yana yiwa Malamai bayani don su ji dadi tunda shine ya kashe wanda suke ƙiyayya dasu. Amma dai wani daga cikin mahalarta taron ya tabbatar mana da cewa kalaman na El-Rufa’i da yayi akan Sheikh Zakzaky ya bar baya da ƙura, inda bayan fitowa daga taron ya ji wasu Mahalarta taron suna ta nuna rashin dacewar wannan kalaman da El-Rufa’i ya yi. Har an ji wani yana fadin cewa “Lallai kuma sai Allah ya rusa ku nan kusa kamar yadda kuka rusa musu makaranta, tunda mu dama kun mana karya da sunan sun tare Hanya ne, ashe dama shiri kuka yi”. Lallai an tabbatar mana cewa da yawan Malaman da aka wallahi sun tafi suna guna-guni ne akan maganar na El-Rufa’i.
Shi a tunanin Nasiru El-Rufa’i ya rusa Shi’a a Zaria ne ko? Bai san cewa a ranar da yayi taron a Zaria ba yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzaky din sun gabatar da taro a Zariyan. Har gobe yayi kaɗan ya ruguza Harka Islamiyya a Zaria kaman yanda magabatan shi suka kasa, yanzu Sheikh Zakzaky gaba ya ƙara yi a halin yanzu. Kana kurarin ka rusa shi a gidanka a lokaci guda kuma shi ya samu cigaba zuwa gidan me gidanka kuma a gidan naka ma Da’awar nashi tana cigaba da gudana.
 – Ibrahim Almustapha Saminaka 
– 12/Maris/2023
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like