Advertisements
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a yau, 14 ga Maris, 2023, ta kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfarar yanar gizo.
Image from Facebook |
An damke su ne a unguwar Lugbe da Kubwa da ke birnin Abuja, biyo bayan samun bayanan sirri da ake zarginsu da aikatawa na zamba a yanar gizo.
Fiye da manyan wayoyin hannu guda 25, kwamfutar tafi-da-gidanka 3 da kuma motocin Mercedes CLA250 da C300 daga hannun wadanda ake zargin.
Credit: EFCC Official Facebook